
Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, ne ya bayyana hakan a yau lokacin da ya karɓi bakuncin jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano a fadarsa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sulaiman A. Dederi
Jami’in Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar jindadin alhazai ya fitar ga manema labarai.
Sarkin ya jaddada muhimmancin dawo da tsarin zabar Amirul Hajj na Kasa, wanda zai jagoranci tawagar Najeriya a lokacin aikin Hajji na kowace shekara. Ya ce tsarin Amirul Hajj ya samo asali ne tun zamanin Annabi Muhammad (SAW), wanda ya karfafa nada shugabanni domin jagorantar tafiya mai tsarki irin ta Hajji.
Ya nanata bukatar sake nada Amirul Hajj na Kasa a matsayin wani muhimmin bangare na aikin Hajji da ya zama na dindindin.
A nasa bangaren, Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya ce sun kai ziyara fadar sarki ne domin gayyatar Mai Martaba zuwa taron karshe na gwajin aikin Hajji da za a gudanar a sansanin Hajji.
Alhaji Lamin Rabi’u ya kara da cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin fara jigilar alhazai zuwa kasa mai tsarki, wanda za a fara ranar 13 ga Mayu, 2025.
Shima a jawabinsa, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya nuna godiya matuka ga Mai Martaba, Malam Muhammad Sanusi II, bisa sadaukarwarsa da jajircewarsa wajen kula da jin daɗin alhazai ‘yan Najeriya. Haka kuma ya goyi bayan kiran da ake yi na neman Gwamnatin Tarayya ta dawo da mukamin Amirul Hajj na Kasa.