
Jami’an tsaro a jihar Borno sun kama malamin da aka hango a wani bidiyo yana cin zarafin Almajirin sa ta hanyar dukan kawo wuka.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ne ya ba da umarnin kama malamin tsangayar, Bukar Modu, da ke unguwar Umarari da ke Maiduguri, inda ya buƙaci a gurfanar da shi bisa zargin cin zarafi.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci duk wani nau’i na cin zarafi ko zaluntar yara ba, adan haka ya baiwa hukumomin tsaro umarnin ɗaukar matakin gaggawa don gurfanar da wanda ya aikata wannan laifi a gaban kotu.
Haka kuma Gwamna Zulum ya gana da yaron da aka ci zarafin, Bashir Gaji, harma ya bashi kyautar gida da tallafin karatu domin taimaka ma sa wajen cigaba da karatun sa, sakamakon iyayen Bashir su na zaune ne a sansanin ‘yan gudun hijira a Monguno bayan rasa mahaifin sa a rikicin Boko Haram.
A karshe ya umarci Ma’aikatar harkokin mata da ci-gaban al’umma, ta tsara shirye-shiryen wayar da kan al’umma don ilmantar da iyalai da malamai kan haƙƙin yara.