Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Nigeriya Zagon Kasa EFCC ta tsare tsohon Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Roni, Gwiwa, Kazaure da Yankwashi Muhammad Gudaji Kazaure bayan da ta gayyace shi zuwa ofishinta da ke Kano inda daga bisani ta tsare shi.
Rahotanni sun ce a yanzu haka ma za’a dauke shi a jirgin sama zuwa Abuja.
EFCC dai tana neman bayanan wasu kyaututtukan kudade naira miliyan 14 da suka shiga asusun bankin tsohon dan majalisar a wani lokaci a shekarar 2019.
To Amma jaridar Daily Nigerian ta ce wasu majiyoyi a EFCC sun ce ana zargin Gudaji Kazauren da karbar Naira miliyan 70 daga wajen tsohon gwamnan Bankin Nigeriya CBN, Godwin Emefiele.
Add A Comment